12 Idanunsa za su yi ja wur saboda shanruwan inabi,Haƙoransa kuma su yi fari fatsaboda shan madara.
13 “Zabaluna zai zauna a gefen teku,Zai zama tashar jiragen ruwa,Kan iyakarsa kuma zai kai harSidon.
14 “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,Ya kwanta a miƙe tsakaninjakunkunan shimfiɗa.
15 Saboda ya ga wurin hutawa ne maikyau,Ƙasar kuma mai kyau ce,Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa dominɗaukar kaya,Ya zama bawa, yana yin aiki maiwuya.
16 “Dan zai zama mai mulki gamutanensaKamar ɗaya daga cikin kabilanIsra'ila.
17 Dan zai zama maciji a gefen hanya,Zai zama kububuwa a gefen turba,Mai saran diddigen dokiDon mahayin ya fāɗi da baya.
18 Ina zuba ido ga cetonka, yaUbangiji.