25 Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek.
26 Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
27 Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.
28 Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,
29 ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.”
30 Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
31 Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba'in da bakwai, ya rasu.