11 Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina.
12 Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.
13 Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.
14 Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro.
15 Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba'in da biyar, tsayinsa ƙafa arba'in da biyar.
16 Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.
17 Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.