5 Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
6 Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya.
7 Nuhu da 'ya'yansa da matarsa, da matan 'ya'yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana.
8 Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa,
9 biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu.
10 Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.
11 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.