1 Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, kowanne da iyalinsa.
2 Su ne Ra'ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza,
3 da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu,
4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru.
5 Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.
6 Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan 'yan'uwansa na wannan tsara.
7 Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.