3 da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu,
4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru.
5 Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.
6 Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan 'yan'uwansa na wannan tsara.
7 Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.
8 A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba.
9 Sai ya ce wa mutanensa, “Duba, jama'ar Isra'ila sun cika yawa sun fi ƙarfinmu.