41 A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.
42 Daren nan da Ubangiji ya sa domin ya fito da Isra'ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra'ilwa su kiyaye domin su girmama Ubangiji dukan zamanansu.
43 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Wannan ita ce ƙa'idar Idin Ƙetarewa, baƙo ba zai ci ba.
44 Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.
45 Amma da baƙo da wanda aka yi ijararsa ba zai ci shi ba.
46 A gidan da aka shirya, nan za a ci, kada a fitar da naman waje, kada kuma a karye ƙashinsa.
47 Dukan taron jama'ar Isra'ila za su kiyaye Idin Ƙetarewa.