1 Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,“Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.
2 Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,Shi ne wanda ya cece ni.Wannan ne Allahna, zan yabe shi,Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
3 Ubangiji mayaƙi ne,Yahweh ne sunansa.
4 “Karusan Fir'auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar,Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.
5 Rigyawa ta rufe su,Suka nutse cikin zurfi kamar dutse.
6 Ya Ubangiji dantsen damanka, mai iko ne,Ya Ubangiji, dantsen damanka ya ragargaza magabta.