3 Yetro kuma ya kawo 'ya'yanta biyu maza, Gershom da Eliyezer tare da ita. Gama Musa ya ce, “Ni baƙo ne a baƙuwar ƙasa.” Saboda haka ne ya raɗa wa ɗaya daga cikin 'ya'yansa, suna, Gershom.
4 Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir'auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer.
5 Sai Yetro ya kawo wa Musa 'ya'yansa maza da matarsa a cikin jeji inda suka yi zango kusa da dutsen Allah.
6 Aka faɗa wa Musa, “Ga surukinka, Yetro, yana zuwa wurinka da matarka da 'ya'yanta biyu tare da ita.”
7 Musa kuwa ya fita ya marabce shi, ya sunkuya, ya sumbace shi. Suka gaisa, suka tambayi lafiyar juna, sa'an nan suka shiga alfarwa.
8 Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.
9 Yetro kuwa ya yi murna saboda alherin da Ubangiji ya yi wa Isra'ilawa da yadda ya cece su daga hannun Masarawa.