7 “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.
8 “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki.
9 Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida,
10 amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku.
11 Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
12 “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
13 “Kada ka yi kisankai.