22 A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”
23 “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
24 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.
25 Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.
26 Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin.
27 Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin.
28 Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin.