1 “Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.
2 Tsawon kowane labule zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida.
3 Labule biyar biyar, za a harhaɗa, a ɗinka.
4 Ku kuma yi wa labulen nan biyu hantuna na shuɗi a karbunsu na bisa.