8 da teburin da kayayyakinsa, da alkuki na zinariya tsantsa tare da dukan kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,
9 da bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa,
10 da saƙaƙƙun tufafi, wato da tsarkakakkun tufafin Haruna da na 'ya'yansa maza domin aikin firistoci,
11 da man keɓewa, da turaren nan mai ƙanshi domin Wuri Mai Tsarki. Za su yi su duka kamar yadda na umarce ka.”
12 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
13 “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.
14 Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama'arsa.