13 Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka, ka kuma tuna, wannan al'umma jama'arka ce.”
14 Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”
15 Musa kuwa ya ce masa, “In ba za ka tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.
16 Yaya zan sani ko na sami tagomashi a wurinka, ni da jama'arka, in ba ka tafi tare da mu ba? Yaya ni da jama'arka, za a bambanta mu da sauran jama'ar da suke a duniya?”
17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”
18 Musa kuwa ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini kanka.”
19 Sai Ubangiji ya ce masa, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda nā yi wa alheri, in nuna jinƙai ga wanda nā yi wa jinƙai.”