1 Sai Musa ya tattara dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi.
2 Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi.
3 Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”
4 Musa kuma ya ce wa taron jama'ar Isra'ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta,
5 ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla,