5 Ubangiji ya ce,“Ka duba cikin al'umman duniya! Ka gani!Ka yi al'ajabi! Ka yi mamaki!Gama zan yi aiki a kwanakinka,Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.
6 Ga shi, ina tā da Kaldiyawa,Al'umman nan mai zafi, mai fitina,Waɗanda suke tafiya ko'ina a duniya,Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.
7 Suna da bantsoro da firgitarwa.Adalcinsu da ikonsu sun danganta ga yadda suke so.
8 “Dawakansu sun fi damisa sauri,Sun fi kyarketan maraice zafin hali,Sojojin dawakansu suna zuwa a guje.Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa,Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.
9 “Sun zo don su yi kama-karya.Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo.Sun tattara bayi kamar yashi.
10 Sukan yi wa sarakuna ba'a,Sukan mai da masu mulki abin wasa.Kowace kagara abin dariya ce a wurinsu,Sukan tsiba ƙasa, su hau, su cinye ta.
11 Sukan wuce da sauri kamar iska,Su yi tafiyarsu.Su masu laifi ne,Ƙarfinsu shi ne gunkinsu.”