1 Zan tsaya a wurin tsayawata,In zauna kuma a kan hasumiya,In jira in ji abin da zai ce mini,Da abin da zai amsa a kan kukata.
2 Sai Ubangiji ya ce mini,“Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna,Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.
3 Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa,Yana gaggautawa zuwa cikarsa,Ba zai zama ƙarya ba.Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri,Hakika zai zo, ba zai makara ba.
4 Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi,Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.