1 Addu'ar nasara wadda annabi Habakuk ya yi.
2 Ya Ubangiji, na ji labarinka,Sai tsoro ya kama ni.Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu,Ayyukan da ka saba yi.Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.
3 Daga Edom Allah ya zo,Daga dutsen Faran Mai Tsarki yake tahowa.Ɗaukakarsa ta rufe sammai,Duniya kuwa ta cika da yabonsa.
4 Walƙiyarsa kamar hasken rana ce,Haske yana haskakawa daga gare shi,A nan ne ya lulluɓe ikonsa.
5 Annoba tana tafe a gabansa,Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.
6 Ya tsaya, ya auna duniya,Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya.Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe,Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya.Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.
7 Na ga alfarwan Kushan suna cikin azaba,Labulen ƙasar Madayana suna rawar jiki.