12 Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa'ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina?
13 Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.
14 Ina ƙin bukukuwanku na amaryar wata, da na tsarkakan ranaku. Sun zama nawaya wadda na gaji da ita.
15 “Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
16 Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta.
17 Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”
18 Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.