18 Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.
19 Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwan da ƙasa take bayarwa.
20 Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”
21 Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.
22 Ya Urushalima, dā kamar azurfa kike, amma yanzu ba ki da amfani, dā kamar kyakkyawan ruwan inabi kike, amma yanzu baƙin ruwa ne kaɗai.
23 Shugabanninku 'yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari'a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.
24 Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra'ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.