5 Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.
6 Kyarketai da tumaki za su zauna tare lafiya.Damisoshi za su kwanta tare da 'yan awaki.'Yan maruƙa da kwiyakwiyan zaki za su yi kiwo tare,Ƙananan yara ne za su lura da su.
7 Shanu da beyar za su yi kiwo tare,'Yan maruƙansu da kwiyakwiyansu za su kwanta lafiya.Zaki zai ci ciyawa kamar sā.
8 Jariri zai yi wasa kusa da maciji mai mugun dafiAmma ba zai cuta ba.
9 A kan Sihiyona, dutse tsattsarka,Ba wani macuci ko mugu.Ƙasar za ta cika da sanin UbangijiKamar yadda tekuna suke cike da ruwa.
10 Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
11 A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku.