3 Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama'ar Isra'ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi.
4 Sa'ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba'a.Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba!
5 Ubangiji ya ƙare mulkin mugun,
6 wanda yake zaluntar jama'a a husace, bai taɓa daina tsananta wa al'ummai ba, wanda ya ci da yaƙi.
7 Yanzu magana ta ƙare, duniya duka tana jin daɗin hutawa da salama. Kowa na ta raira waƙar murna.
8 Itatuwan fir da itatuwan al'ul na Lebanon suna murna da faɗuwar sarkin! Ba wanda zai tasar musu da sara!
9 “Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu.