9 Za a ƙasƙantar da kowane mutum, a kunyata shi. Kada ka gafarta musu, ya Ubangiji!
10 Za su ɓuya a cikin kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa!
11 Rana tana zuwa sa'ad da girmankan 'yan adam zai ƙare, zai kuma lalatar da fāriyar 'yan adam. Sa'an nan Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka.
12 A wannan rana, Ubangiji Mai Runduna zai ƙasƙantar da kowane mai iko, da kowane mai girmankai, da kowane mai fāriya.
13 Zai hallaka dogayen itatuwan al'ul na Lebanon, da dukan itatuwan oak na ƙasar Bashan.
14 Zai baje duwatsu da tuddai masu tsayi,
15 da kowace doguwar hasumiya, da ganuwar kowace kagara.