11 Wannan shi ne jawabi a kan Edom.Wani daga Edom ya kira ni ya ce, “Ya mai tsaro, gari ya kusa wayewa? Ka gaya mini har sai yaushe zai waye?”
12 Sai na amsa na ce, “Gari zai waye, amma za a sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin tambaya, sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”
13 Wannan shi ne jawabi a kan Arabiya.Ya ku jama'ar Dedan, waɗanda ayarorinku suka yi zango a ƙasar Arabiya wadda take faƙo,
14 ku ba jama'a waɗanda suka zo gare ku masu jin ƙishi ruwa su sha. Ya ku jama'ar ƙasar Tema, ku ba 'yan gudun hijira abinci.
15 Mutane suna gudu don su tsere wa takuban da za su kashe su, da bakkunan da za su harbe su, su kuma tsere wa dukan hatsarorin yaƙi.
16 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Saura shekara ɗaya tak girman kabilar Kedar zai ƙare.
17 Jarumawan Kedar su ne maharba, amma sai kaɗan za su ragu daga cikinsu, ni, Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”