1 Wannan shi ne jawabi a kan Taya.Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.
2 Ku yi kuka ku fataken Sidon! Kun aika da mutane
3 a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al'umma.
4 Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar 'ya'ya ba, ban taɓa goyon 'ya'ya mata ko maza ba.”