4 Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar 'ya'ya ba, ban taɓa goyon 'ya'ya mata ko maza ba.”
5 Har Masarawa ma za su firgita su razana, sa'ad da suka ji, cewa an hallakar da Taya.
6 Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama'ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish!
7 Ya yiwu kuwa a ce wannan Taya ce birnin farin ciki, wadda aka kafa ta tuntuni? Wannan kuwa ita ce birnin da yake aikawa da mutane hayin teku su kafa nahiyoyi?
8 Wane ne wannan wanda ya shirya ya aukar wa Taya da wannan duka, wannan muhimmiyar alkarya, wadda fatakenta hakimai ne, waɗanda ake ɗaukaka su fiye da sauran mutane a duniya?
9 Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.
10 Ku je ku nomi ƙasarku jama'ar nahiyoyin Tarshish! Ba wanda zai ƙara kiyaye ku.