3 Duniya za ta ragargaje ta zama kufai. Ubangiji ne ya faɗa, haka kuwa za a yi.
4 Duniya za ta bushe ta ƙeƙashe, duniya duka za ta raunana, duniya da sararin sama za su ruɓe.
5 Jama'ar sun ƙazantar da duniya da suka keta dokokin Allah, suka ta da alkawarin da ya yi don ya dawwama.
6 Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai.
7 Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi,
8 kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare.
9 Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi.