1 Bagaden Allah, Urushalima kanta, ƙaddara ta auko mata! Birnin da Dawuda ya kafa zango, ƙaddara ta auko mata! Bari shekara ɗaya ko biyu su zo su wuce suna shagulgulansu, suna bukukuwansu,
2 sa'an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!
3 Allah zai tasar wa birnin, ya kewaye shi da yaƙi.
4 Urushalima za ta zama kamar fatalwar da take ƙoƙarin yin magana daga ƙarƙashin ƙasa, guni yana fitowa daga turɓaya.
5 Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,
6 Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta.
7 Sa'an nan dukan sojojin sauran al'umman da suka fāɗa wa birni inda bagaden Allah yake da yaƙi, da dukan makamansu, da kayayyakin yaƙinsu, kome da kome za su shuɗe kamar mafarki, kamar tunanin dare.