16 Sun birkitar da kome! Wane ne ya fi muhimmanci, mai ginin tukwane ko yumɓun? Abin da mutum ya yi da hannunsa ya iya ce wa mutumin, “Ba kai ka yi ni ba”? Ko kuma zai iya ce masa, “Ai, ba ka san abin da kake yi ba”?
17 Kamar yadda karin maganar ta ce, kafin a jima kurmi zai zama gona, gona kuma za ta zama kurmi.
18 A wannan rana, kurame za su ji sa'ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani.
19 Matalauta da masu tawali'u za su sāke samun farin ciki wanda Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya bayar.
20 Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi.
21 Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari'ar adalci.
22 Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya fanshi Ibrahim daga wahala, ya ce, “Jama'ata, ba za a ƙara kunyatar da ku ba, fuskokinku ba za su ƙara yanƙwanewa don kunya ba.