26 Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa'ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.
27 Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.
28 Ya aika da iska a gabansa kamar rigyawa wadda take kwashe kome, ta tafi da shi. Yakan gwada al'ummai ya kai su hallaka, yakan sa dukan shirye-shiryensu na mugunta su ƙare.
29 Amma ku, jama'ar Allah, za ku yi farin ciki, ku raira waƙa kamar yadda kukan yi a daren tsattsarkan idi. Za ku yi murna kamar waɗanda suke tafiya suna bushe-bushe a hanyarsu ta zuwa Haikalin Ubangiji Mai Tsarki, Mai Ceton Isra'ila.
30 Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
31 Assuriyawa za su firgita sa'ad da suka ji muryar Allah, suka kuma ji irin zafin hukuncinsa.
32 Sa'ad da Ubangiji ya miƙa sandan hukuncinsa ya yi ta bugun Assuriyawa, jama'arsa kuwa za su yi ta kaɗa ganguna da garayu, su yi murna!