1 Magabtanmu sun shiga uku! Sun yi fashi sun ci amana, ko da yake ba wanda ya yi musu fashi ko cin amana. Amma lokacinsu na fashi da na cin amana zai ƙare, su ne kuma za a yi wa fashi da cin amana.
2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai. Muna sa zuciyarmu gare ka. Ka dinga kiyaye mu yau da gobe, ka kuma cece mu a lokatan wahala.
3 Lokacin da kake yaƙi dominmu, al'ummai sukan gudu daga bakin dāga.
4 Akan tsirga a bisa abubuwan da suke da su, a kwashe su ganima.
5 Ubangiji da girma yake! Yana mulki a kan kome. Zai cika Urushalima da adalci da mutunci,