17 Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa.
18 Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare.
19 Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba!
20 Ku duba Sihiyona, birni inda muke idodinmu. Ku duba Urushalima! Za ta zama wurin zama mai lafiya! Za ta zama kamar alfarwar da ba ta taɓa gusawa ba, wadda ba a taɓa tumɓuke turakunta ba, igiyoyinta kuma ba su taɓa tsinkewa ba.
21 Ubangiji zai nuna mana ɗaukakarsa. Za mu zauna a gefen koguna da rafuffuka masu faɗi, amma ba kuwa jirgin ruwan abokan gāba da zai bi ta cikinsu.
22-23 Dukan kayayyakin waɗannan jiragen ruwa ba su da amfani, tafiyarsu ba za ta yi nisa ba! Za a kwashe dukan dukiyar sojojin abokan gāba. Za ta yi yawa har sauran jama'a za su sami rabonsu. Ubangiji kansa shi zai zama sarkinmu, zai mallake mu, ya kiyaye mu.
24 Ba wanda zai zauna a ƙasarmu har ya ƙara yin kukan yana ciwo, za a kuma gafarta dukan zunubai.