1 A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”
2 Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu'a, ya ce,
3 “Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.
4 Sa'an nan Ubangiji ya umarci Ishaya,
5 cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.
6 Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”