1 Ubangiji ya ce,“Ka ta'azantar da jama'ata.Ka ta'azantar da su!
2 Ka ƙarfafa jama'ar Urushalima.Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa,Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu.Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”
3 Murya tana kira tana cewa,“Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji!Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!
4 Za a cike kowane kwari,Za a baje kowane dutse.Tuddai za su zama fili,Ƙasa mai kururrumai za ta zama sumul.
5 Sa'an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji,Dukan 'yan adam kuwa za su gan ta.Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”