1 Allah ya ce,“Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe!Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari'a.Za ku sami zarafi ku yi magana.Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.
2 “Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas,Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi?Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai?Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura!Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!
3 Yana biye da kora, yana kuma tafiya lafiya,Da sauri ƙwarai, da ƙyar yake taɓa ƙasa!
4 Wane ne ya sa wannan ya faru?Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi?Ni Ubangiji, ina can tun da farko,Ni kuma Ubangiji Allah,Zan kasance a can har ƙarshe.