1 Ubangiji ya ce,“Ga bawana, wanda na ƙarfafa,Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa.Na cika shi da ikona,Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.
2 Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba,Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.
3 Zai lallaɓi marasa ƙarfi,Ya nuna alheri ga tafkakku.Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.
4 Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba,Zai kuma kafa gaskiya a duniya,Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”