10 “Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna,Na zaɓe ku al'umma, baiwata,Domin ku san ni, ku gaskata ni,Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah.In banda ni ba wani Allah,Ba a taɓa yin wani ba,Ba kuwa za a yi ba.
11 “Ni kaɗai ne Ubangiji,Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.
12 Na faɗi abin da zai faruSa'an nan na zo domin taimakonku.Ba wani gunkin da ya taɓa yin haka,Ku ne shaiduna.
13 Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur,Ba wanda zai iya tserewa daga ikona,Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”
14 Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce,“Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila,Zan rushe ƙofofin birni,Sowar mutanen birnin za ta zama kuka.
15 Ni ne Ubangiji, Allahnku Mai Tsarki na Isra'ila,Ni na halicce ku, ni ne kuma sarkinku.”
16 Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku,Da turba kuma a cikin ruwa.