25 Na sa masu duba su zama wawaye,Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari.Na bayyana kuskuren maganar masu hikima,Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.
26 Amma sa'ad da bawana ya yi annabci,Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena,Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika.Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can,Za a kuma sāke gina biranen Yahuza.Waɗannan birane za su daina zama kufai.
27 Na yi umarni na sa teku ta ƙafe.
28 Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina,Za ka yi abin da nake so ka yi,Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima,A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”