1 “Wannan ne ƙarshen allolin Babila!Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada,Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna,Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!
2 Wannan ne ƙarshen waɗannan alloli,Gumaka ba su iya ceton kansu,Aka kame su aka tafi da su.
3 “Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu,Dukanku, mutanena da kuka ragu.Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.
4 Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku,Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura.Ni na halice ku zan kuwa lura da ku,Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”
5 Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni?Akwai wani mai kama da ni?
6 Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya,Suna auna azurfa a kan ma'auni.Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki,Sa'an nan suka rusuna suka yi masa sujada!