1 Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila,Ku da kuke zuriyar Yahuza.Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji,Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila,Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.
2 Amma duk da haka kuna fāriya, da cewaKu ne mazaunan birni mai tsarki,Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila,Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.
3 Ubangiji ya ce wa Isra'ila,“Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru,Sa'an nan na sa ya faru ba labari!
4 Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne,Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.
5 Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku,Na hurta abubuwa tun kafin su faru,Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su,Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.