3 Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu,In sa ya zama makoki domin matattu.”
4 Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa,Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi.A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini.
5 Ubangiji ya ba ni fahimi,Ban kuwa yi masa tayarwa baKo in juya in rabu da shi.
6 Na tsiraita ga masu dūkana.Ban hana su sa'ad da suke zagina ba,Suna tsittsige gemuna,Suna tofa yau a fuskata.
7 Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba,Gama Ubangiji Allah yana taimakona.Na ƙarfafa kaina domin in jure da su.Na sani ba zan kunyata ba,
8 Gama Allah yana kusa,Zai tabbatar da ni, marar laifi ne,Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni?Bari mu je ɗakin shari'a tare!Bari ya kawo ƙararrakinsa!
9 Ubangiji kansa zai kāre ni,Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne?Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe,Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!