1 Ubangiji ya ce,“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku,Ku da kuka zo gare ni neman taimako.Ku yi tunanin dutse inda kuka fito,Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.
2 Ku yi tunani a kan kakanku Ibrahim,Da Saratu, wadda kuke zuriyarta.Sa'ad da na kira Ibrahim ba shi da ɗa,Amma na sa masa albarka, na ba shi 'ya'ya,Na sa zuriyarsa suka yi yawa.
3 “Zan ji juyayi a kan Sihiyona,Da dukan masu zama a kufanta.Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu,Kamar lambun da na dasa a Aidan.Murna da farin ciki za su kasance a can,Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.
4 “Ku kasa kunne gare ni, ku mutanena,Ku saurara ga abin da nake faɗa,Na ba da koyarwata ga al'ummai,Dokokina za su kawo musu haske.