17 Ya Urushalima, ki farka!Ki tashi da kanki, ki miƙe!Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha,Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!
18 Ba wanda zai yi miki jagora,Ba wani daga cikin mutanenkiDa zai kama hannunki.
19 Masifa riɓi biyu ta auko miki,Yaƙi ya lalatar da ƙasarki,Mutanenki suka tagayyara da yunwa.
20 A kan kusurwar kowane titiMutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi,Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama.Suka ji ƙarfin fushin Allah.
21 Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala,Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,
22 Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce,“Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina.Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.
23 Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku,Su waɗanda suka sa kuka kwanta a titunaSuka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”