12 A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba,Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba!Ubangiji Allah ne zai bishe ku,Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.
13 Ubangiji ya ce,“Bawana zai yi nasara a aikinsa,Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.
14 Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi,Ya munana har ya fita kamannin mutum.
15 Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa,Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki.Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”