3 Ubangiji ya ce wa jama'arsa,“Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba,Amma ga shi, kuka zama bayi.Ba za a biya kuɗin fansa domin a 'yantar da ku ba,Amma, ga shi, za a 'yantar da ku.
4 Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar,Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.
5 Yanzu kuma, ga shi, yana faruwa a Babila,Kuka zama kamammu a can, ba gaira ba dalili.Su da suke mulkinku suna girmankai, suna fāriya,Suna ta nuna mini raini.
6 Amma zuwa gaba za ku saniNi ne Allah, wanda na yi magana da ku.”
7 Me ya fi wannan kyau?A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu,Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama.Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona,“Allahnki sarki ne!”
8 Waɗanda suke tsaron birni suna sowa,Suna sowa tare saboda murna!Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!
9 Ku ɓarke da sowar murna,Ku kufan Urushalima!Ubangiji ya ta'azantar da jama'arsa,Ya fanshi birninsa.