8 Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci,Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.”Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.
9 “Na yi alkawari a zamanin Nuhu,Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba.Yanzu kuwa ina miki alkawari,Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba,Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.
10 Duwatsu da tuddai za su ragargaje,Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam.Zan cika alkawarina na salama har abada.”Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.
11 Ubangiji ya ce,“Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke.Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.
12 Zan gina hasumiyarki da jan yakutu,Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta,Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu'ulu'ai.
13 “Ni kaina zan koya wa mutanenki,Zan kuwa ba su wadata da salama.
14 Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki.Za ki tsira daga shan zalunci da razana.Gama ba za su kusace ki ba.