10 “Maganata kamar dusar ƙanƙara take,Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya.Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba,Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.
11 To, haka maganar da na faɗa take,Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata,Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.
12 “Za ku fita daga cikin Babila da murna,Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama.Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa,Itatuwa za su yi ta sowa don murna!
13 Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu,Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa.Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada,Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”