1 Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala'i.
2 Ya shiga da salama yana hutawa a kabarinsa, shi wanda ya yi tafiya da adalci.
3 Amma ku ku matso nan kusa, ku 'ya'ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa.
4 Wa kuke yi wa ba'a? Ga wa kuke wage baki, kuna zaro harshe? Ashe, ku ba 'ya'yan masu laifi ba ne, zuriyar marikita,
5 ku da muguwar sha'awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe 'ya'yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi?