13 Sa'ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.”
14 Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama'ata!”
15 Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.
16 Ba zan yi ta gāba da ku, ko in yi ta fushi da ku har abada ba. Gama ruhu zai yi suma a gabana, da numfashin su waɗanda na halitta.
17 Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.
18 “Na ga al'amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta'azantar da su tare da masu makoki.
19 Salama, salama,” in ji Ubangiji, “Ga wanda yake nesa da wanda yake kusa. Zan warkar da su.