8 A bayan ƙofa da madogaran ƙofa kuka kafa gumakanku. Kun rabu da ni, kun kware gadonku, kuna hau kun fāɗaɗa shi, kuka ƙulla yarjejeniya tsakaninku da su. Kuna ƙaunar gadonsu, kun dubi tsiraici.
9 Kun tafi wurin Molek da mai, da turare iri iri da kuka riɓaɓɓanya. Kun aika jakadunku can nesa, kun aike su su gangara, har zuwa lahira.
10 Kun damu saboda nisan hanyarku, amma ba ku ce, “Ba shi da wani amfani ba.” Ƙarfinku ya sake sabunta ranku, don haka ba ku suma ba.
11 Ubangiji ya ce, “Wa ya sa ku fargaba, kuke jin tsoronsa, har kuka yi ƙarya? Ba ku tuna da ni, ko ku kula da ni ba? Ashe, ban yi haƙuri tun da daɗewan nan ba, duk da haka kuwa ba ku ji tsorona ba?
12 Zan ba da labarin adalcinku da ayyukanku, amma ba za su taimake ku ba.
13 Sa'ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.”
14 Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama'ata!”